Matsalolin Najeriya Sun Fi Ƙarfin APC – Saraki

Tsohon Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ce, matsalar Najeriya ta fi ƙarfin jam’iyyar APC ita kaɗai, saboda haka kuskure ne ace za’a bar ma jam’iyyar warware matsalolin Najeriya ita kadai.

Saraki wanda shi ne ke jan ragamar kwamitin sasantawa na jam’iyyar PDP, ya nuna cewa akwai bukatar hada hannu da ‘yan hamayya domin lalubo mafitar da za a yi maganin matsalolin Najeriya baki daya, musammam a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Saraki ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a dakin karatunsa na Abeokuta da ke jihar Ogun.

Tsohon shugaban Majalisar ya ce, “Idan muna maganar akan garkuwa da mutane, abin da ake bukata shi ne gwamnati da samar da shugabancin da zai kira wo duka masu ruwa da tsaki. mu zo a tattauna muga yadda za a shawo kan wannan matsaloli.”

Labarai Makamanta