Matsalolin Najeriya: Bana Tausayin Buhari – Bisi Akande

Labarin dake shigo mana daga Birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Tsohon Shugaban jam’iyyar APC Cif Bisi Akande, ya bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari dalilin da yasa bai tausayinsa bisa caccakarsa da yan Najeriya ke yi kan rashin tsaro.

Tun bayan hawan Shugaba Buhari kan karagar mulki a 2015, matsalar tsaro a Najeriya ta tashi da yaki da Boko Haram zuwa rikicin makiyaya da manoma, yanzu kuma garkuwa da mutane.

Bisi Akande ya bayyana wa Buhari cewa ai shi ya nemi zama shugaban kasa saboda haka ya magance matsalar, ya sauke nauyin dake kafadunsa.

Akande ya yi jawabi ne yayin bikin kaddamar da littafin rayuwarsa da ya gudana ranar Alhamis, 9 ga Disamba a Eko Hotel and Suites, Victoria Island, Lagos.

“Mun san kana son kasar, amma muna son zaman lafiya a kasar nan, kuma muna son cigaba. Muna zaginka kan komai da ke faruwa da kasar.” “Mun san mu macuta ne, kuma laifinmu ne amma muna daura maka. Bana tausayinka saboda kai ka nemi aiki.”

Labarai Makamanta