Matsalolin Arewa: Laifin ‘Yan Arewa Ne – Bala Buhari

Arewacin kasar nan shine yankin da yafi ko wani yanki a fadin kasar nan girma, mutane, albarkatun kasa da sauransu amma kuma shine yankin da yafi kowanne koma baya a yanzu. Alkaluma da dama sun nuna cewa arewa tafi kowani yanki a kasar nan yawan yaran da basa zuwa makaranta, arewa ne ke kan gaba a matsalolin tsaro, arewa ne ake fama da talauci duk da fadin kasar noma da muke dashi.

Malam Bala Buhari mai sharhi ne akan al’amuran yau da kullum kuma ya kasance bako a cikin shirin INA DALILI wanda ake gabatar dashi a gidan talbijin da rediyo na Liberty TV dake kaduna. A cikin shirin ya tabo abubuwan da suka kawo wa yankin arewa koma baya a kowani fanni, da yake bayani akan matsalar tsaro, Bala Buhari yace akwai rawar da mutanen arewa suka taka sosai wurin lalacewar tsaro a wannnan yankin, inda ya bada misali da cewa” a arewa ne zaka ga uba baisan inda ‘dansa yake kwana ba, baisan inda yake samun abinci ba balantana harkan ilimin sa. Wannnan nauyi ne da ya wajjaba akan iyaye ba gwamnati ba. Sannnan ya zama wajibi ‘yan arewa su zauna su fara lalubo hanyoyin kawo karshen wannnan matsalar na tsaro wanda a baya saidai muji labari a makota amman yanzu yashigo mana da wasu salo kala kala.

Da yake magana akan harkar shugabanci da cigaban yankin, Malam Bala yace ” a jamhoriya ta daya lokacin su Sardauna,Tafawa Balewa da su Janar Hassan Usman Katsina lokacin burin su kawai a lokacin cigaban arewa kuma sun taimaki kowa ba tare da duba addinin shi ba ko kabilar da ya fito, muddin kai dan arewa ne zasu yi iya bakin kokarin su akan ka. Amma tun bayan su sai muka dinga samun shuwagabanni wanda ba irin manufofin su suke dashi ba. Yace idan ka duba yanda suka gudanar da ayyuka a wanchan lokacin duk da babu man fetur a kasar ma a lokacin amman da yake suna da hangen nesa har yanzu ana cin moriyar ayyukan su inda ya bada misali da manyan asibitocin da ke arewa da kuma jami’ar Ahmadu Bello dake zaria.

A lokacin rayuwar su sun sadaukar da kansu ne wurin cigaban yankin arewa . Bayan su an sami wasu shuwagabannin amman babu wani abin da zaka iya nunawa a kasa kace gashi sune sukayi a lokacin su wurin cigaban arewa. Hatta babban birnin tarayya dan arewa yai sanadiyyar dawowar ta abuja amma a yanzu saboda keta da son zuciya irin namu na yan arewa inda zaka duba manyan gidajen dake abuja zakaga duk yan kudu ne suka mallake su.

Daya ke amsa tanbaya akan ta yaya arewa zata iya dawowa ta amsa sunan ta na jagora koda a nan gaba? Malam Bala yace yanzu sau nawa Buhari na tsayawa takara a kasar nan baya nasara har saida ya hada kai da wani yanki kamin yai nasarar zama shugaban kasa. Muna da yawa amman bamu da hadin kai, sannnan saboda lalacewar mu da kuma kowa na ganin ya isa har yasa yanzu bamu da mutum daya dazai iya tsawatar damu a arewa. Wanda ba karamin matsala bane a ce mu keda yawa amman koda jagora bamu dashi. Kuma idan babu hadin kai babu yanda zamu iya fuskantar shuwagabanninmu domin su kawo mana gyara

Zaku iya kallon cikakken hirar a wannnan shafin namu dake kasa👇🏿

Related posts