Matsalar ‘Yan Bindiga: Na Zama Dan Kallo – Dr Gumi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar gitaccen malamin Addinin musulunci, kuma mazaunin jihar Sheikh Ahmed Gumi ya bayyana cewa da ga yanzu ya koma dan kallo, ba zai sake cewa uffan ba ko tattaunawa da ya ke yi da ‘yan bindiga ba saboda a samu zaman lafiya ya dawo tsakanin maharan da kuma hare-hare

Sheikh Gumi ya kasance mai neman a yi sulhu tsakanin gwamnati da ‘Yan bindiga, sai dai kuma a wata hira ta musamman da yayi da manema labarai a Kaduna ya ce daga yanzu ya daina sa baki cikin harkar tun da gwamnati ta aiyanasu a matsayin ‘yan ta’adda.

Babban Shehin ya ce tsakani da Allah yayi iya kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya a yankunan dake fama da tashin hankali amma abin ya ci tura saboda wasu suna yi wa tafiyar kafar ungulu.

A baya dai Gumi ya sha lunkuyawa cikin Daji yana baiwa Yan Bindiga shawarwari a zauna lafiya da juna, ayi sulhu, ya kuma baiwa gwannatin Najeriya shawarwari kan yadda za’a shawo kan lamarin ta hanyar yafewa Yan Bindiga da kuma samarwa Fulani makiyaya abubuwan more rayuwa.

Gumi ya kara da cewa tun daga lokacin da gwamnatin Najeriya ta ayyana Yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda ya yanke shawarar daina shiga tsakanin ‘Yan bindiga da gwannati domin bada shawarwari.

Yace yayi iya yinsa, ” Zan daina sa kaina cikin hatsari, yanzu na zama dan kallo daga gefe, cewar Malam Gumi.

A baya, nayi kasada da rayuwata wajen shiga daji ina ganawa da su domin kawo zaman lafiya a kasata amma hakan bai samu ba, aiki ne mai hatsarin gaske saboda wasu ‘Yan bindigar kiris suke jira suyi harbi, cewar Malam.

Amma alhamdullillah mun shiga cikinsu kuma mun sami Karin illimi Kan yadda ake tafiyar da harkar. Anan gaba idan aka samu wani canjin siyasa a Najeriya zan iya cigaba da aikin da na faro domin kawo zaman lafiya da arziki mai yelwa a kasata, inji sheikh Ahmad Gumi.Tags: AbujaGumiHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMES

Labarai Makamanta