Matsalar Tsaron Kaduna: El Rufa’i Ya Gana Da Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa a Abuja ranar Talata.

Ya samu rakiyar Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna. Bayan ganawar gwamnan da shugaban kasan, wani hoton Gwamna El-Rufai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wanda ya janyo maganganu daga jama’a.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai a gurfane gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bashir Ahmad ya wallafa hoton tare da cewa, “Mallam El-Rufai na Baba Buhari.”

Babu jimawa da saka hoton a Facebook, ‘yan Najeriya suka hau caccaka yayin da wasu suke ta yaba wa gwamnan kan bayyana biyayyarsa da yayi ga shugaban kasan.

Labarai Makamanta