Matsalar Tsaro Zai Haifar Mana Cikas A Babban Zabe – INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa.

Yakubu ya yi wannan furuci ne a wurin taron kwamitin tsaro na haɗin guiwa (ICCES), wanda ya gudana a hedkwatar hukumar INEC dake Abuja ranar Juma’a.

Shugaban INEC ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar Anambra. Sai dai yace yawaitar matsalar tsaro a sassan Najeriya, wata barazana ce kuma abin damuwa game da zaɓen 2023.

“Game da zaben ƙarewar wa’adi, muna da manyan zaɓukan dake tafe cikin wannan shekarar 2022. Zaɓen gwamnan jihar Ekiti zai gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022 da kuma na jihar Osun ranar 16 ga Yuli, 2022.” “Sannan akwai zaben kananan hukumomi na Abuja da za’a gudanar nan gaba kaɗan.

Labarai Makamanta