Matsalar Tsaro Zai Haifar Da Tarnaki A Wasannin Ahmed Musa A Kano Pillars

Shugaban kungiyar Kano Pillars Surajo Yahaya ya tabbatar da cewa sabon ɗan wasan zai iya buga dukkan wasannin gida, amma ba zai halarci yawancin wasannin waje ba dalilin matsalar rashin tsaro.

“Ahmed Musa babban dan wasa ne kuma dubi ga yadda halin tattalin arzikin kasar nan da hanyoyi marasa kyau. Zai buga dukkan wasannin gida kuma idan akwai jirgi a jihar, zai halarci wasannan waje.

A bangare guda, Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyarsa ta wasanni ta miliyoyin naira a Kaduna inda ake sa ran matasa za su samu horo kuma za su iya baje kolin baiwarsu ma.

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Leceister City yana daya daga cikin attajiran yan wasan Najeriya idan aka yi la’akari da kadarorin sa tun lokacin da ya fara wasan kwallon kafa daga titin garin Jos.

Ahmed Musa ya fara wasan kwallon kafa a garin Jos kafin ya koma kungiyar JUTH FC daga inda tsohon zakaran gasar kwallon kafa ta Kano Pillars ya sanya masa hannu.

Labarai Makamanta