Matsalar Tsaro: Ya Zama Dole Jama’a Su Daina Tsoron Mutuwa – Sarkin Musulmi

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III a ranar Alhamis, ya yi Alla-wadai da kisan gillan da ake yiwa matafiya a yankin ƙaramar Hukumar Sabon Birnin Gobir da sauran kashe-kashen da ake yi wa ‘yan Najeriya, musamman a yankin Arewa.

Sarkin yace yan jarida basu ruwaito mafi akasarin kashe-kashen da ake yi a yankin wannan ya sa jama’a ba su san halin da ake ciki ba a yankin.

Ya bayyana hakan a taron majalisar addinai na rubu’in karshen shekarar 2021 da ya gudana a Jihar.

Sarkin Musulmi Abubakar ya yi kira ga Musulmai da Kirista su daina jin tsoron barazanar yan bindiga.

“Lokaci ya yi da ya zama dole jama’a su daina jin tsoron mutuwa su jajirce wajen ganin bayan matsalar tsaro”.

Ya bayyana yadda wasu mutane ke aiko wasika a Zamfara cewa duk wanda aka kama yana zuwa Coci za’a kashe shi. Yace: “Lokacin da na ga takardar da yan bindiga ke yiwa Kiristoci barazana a Zamfara, sai nayi tambaya shin menene aikin jami’an tsaronmu.”

“Ba zan daina zuwa Masallaci ba don wasu sun yi rubuta a takarda cewa idan na shiga Masallaci za’a kashe ni, su kasheni din, dama zan mutu, saboda haka Kiristoci su daina tsoron zuwa Coci saboda wasu na musu barazana.”

Labarai Makamanta