Matsalar Tsaro: Muji Tsoron Allah Domin Samun Mafita – Imam Lau

An kirayi al umma musulmai da su kasance masu sa tsaron Allah madakakin sarki a zukatansu domin samun taimakon Allah wajen neman kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasan nan baki daya.

Shugaban kungiyar Izala ta kasa sheik Abdullah Bala Lau ne yayi wannan kira alokacin da yake gabatar da hudubarsa a wurin Sallar da aka gudanar a Capital School dake yola.

Sheik Bala Lau ya shawarci al umma musulmai da sukasance masu hada kansu a koda yaushe domin ganin an samu zaman lafiya a fadin kasannan baki daya.

Ya kuma kirayi al umma musulmai da suyi amfani da wannan lokaci wajen yin adu o I da kuma sada zumunta domin kawo karshen kalu balen tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta