Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana ɗaruruwan mata sun toshe babbar hanyar zuwa Gusau da Sokoto domin nuna fushi kan halin da suke ciki na hare-haren ƴan bindiga.
Wasu hotuna sun nuna mata da yara ɗauke da kayansu saman hanya dab da shiga garin Tsafe.
Mutanen garin waɗanda mafi yawansu mata ne da yara sun tare babbar hanyar ranar Laraba inda suka haddasa cunkoson ababen hawa.
Wani mazaunin yankin ya ce matan sun tsere wa hare-haren ƴan bindiga ne da suka addabe su, suna masu fyade. Kuma sun toshe hanyar ne domin janyo hankalin gwamnati kan halin da suke ciki.
Zanga-zangar tasu ta sa babu mai iya ratsawa ya fita ko shiga yankin.
Wani direban mota a babbar tashar Gusau ya shaidawa BBC Hausa cewa an shafe awanni babu wani direban da ya shigo tashar daga hanyar Funtua.
Mutanen Zamfara sun shafe makwanni babu hanyoyin sadarwa a sassan jihar da hana cin kasuwannin mako, matakin da hukumomin tsaro suka ce sun ɗauka don magance matsalar ƴan bindiga masu fashi da satar mutane da suka addabi yankin arewa maso yammaci.
You must log in to post a comment.