Matsalar Tsaro: Masu Sukarmu Basa Yi Mana Adalci – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya da su rinƙa yin adalci a duk lokacin da suke sharhi bisa matsalar tsaro inda ya ce su rinƙa kwatantawa da abin da gwamnatinsa ta gada tun a 2015.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da Khalifan Tijjaniyya na duniya ya kai masa ziyara a ranar Juma’a inda shugaban ya bayyana cewa ya kamata jama’a su rinka magana kan irin nasarorin da suka samu a ɓangaren tsaro musamman a arewa maso gabas da kuma kudu maso kudancin ƙasar.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da irin haƙƙoƙin da suka rataya a wuyanta da suka shafi tsaro inda ya ce za su ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinsu.

Shugaban ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su bayar da haɗin kai da kuma nuna goyon baya a harkar tsaro da kuma yaba wa ayyukan da gwamnati ke yi inda ya ce “mun yi iya bakin ƙoƙarinmu kuma za mu ci gaba da yi ta hanyar samar da tsare-tsare masu kyau domin yaƙi da ta’addanci.

Labarai Makamanta