Matsalar Tsaro: Laifin Gwamnoni Ne Ba Shugaban Kasa Ba – Gwamnatin Tarayya

An bayyana cewa matsalar tsaro dake addabar Najeriya a kusan kullum laifin gwamnatocin jihohi ne ba Shugaban ƙasa ba, kuma ya dace jama’a su fahimci haka.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed lokacin da yake mayar da martani dangane da korafin da ‘yan Najeriya ke yi na taɓarɓarewar tsaro a kasar.

Lai Mohammed ya nemi jam’iyyar PDP da ta ga laifin gwamnatocin jihohi, ciki har da wadanda mambobin jam’iyyar ke shugabanta, a kabubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

A cewarsa, ayyukan ‘yan bindiga da ta’addancin masu satar mutane ba laifin gwamnatin tarayya bane, idan aka faɗa bincike da nazari za’a gano gazawar gwamnoni da dama.

In dai jama’a basu mance ba Shugabannin PDP sun yi taron manema labarai a ranar Litinin, inda suka nuna rashin amincewarsu kan irin halin rashin tsaro da ake ciki a kasar tare da neman gwamnatin tarayya ta magance matsalolin gaba daya.

Lai Mohammed, ya ƙara da cewar abin takaici ne yadda jam’iyyar adawa ba ta fahimci kokarin da wannan gwamnati mai ci ke yi a kan lamarin ba ciki har da taron zauren garin da aka gudanar a Kaduna inda aka tsara wani shiri na matakai goma.

Ya ce taron manema labarai na PDP ba komai bane face wasa kawai kuma ya kara zargin jam’iyyar da kokarin siyasantar da batutuwan da suka shafi tsaron kasa.

Labarai Makamanta