Matsalar Tsaro: Izala Ta Bukaci Buhari Ya Sake Damara

Kungiyar wa’azin musulunci mai da’awar kauda cushe cikin addini (BIDI’AH) tare da kokarin tsayar da yin addini kamar yadda Annabi mai tsira da aminci yayi (SUNNAH) tayi kira ga gwamnatin tarayyar Naijeriya da ta kara kokari kan yadda takeyi akan matsalar tsaro da ya addabi arewacin kasar, musamman jihohin Sokoto, Zamfara, Niger, Kaduna da jihar Katsina.

Sakon sanarwar ya fito ne daga shugaban Kungiyar ta kasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau a wata tattaunawa da yayi da ‘Yan jaridu a ofishinsa dake birnin Abuja. Shugaban yayi kira da babban murya ga jami’an tsaro wajen samo sabbin dabaru domin kawo karshen zubar da jinin al’umma tare da murkushe’yan ta’adda a wannan yanki lura da hakikanin wadannan‘Yan ta’adda basu fi karfin jami’an tsaron Naijeriya ba, amma abun kullum Sai gaba-gaba yakeyi, ana ta zubar da jinin al’umma wadanda basuji ba basu gani ba, to a Ina matsalar take?

A cewarsa shehin malamin yace; “Allah ta’ala ya halicci bayi da falalarsa ya bayyana musu daidai daga kuskure, Allah ya haramta zalunci wa kansa, kuma ya sanya ta haramun a tsakanin bayinsa, sannan yace kada kuyi zalunci, domin samar musu da rayuwa mai nagarta. Hakika Al’amarin Amana na jagoranci wajibine Al’umma susani Musulunci yayi fayyacecciyar bayani akayi, wanda yake wajibine Shugaba ya tsare lafiyar Al’umma, rayukansu da dukiyoyinsu. Kuma tabbas Allah zaiyi Hisabi akan wadannan”.

Dan haka ina kira ga jama’a da mu kara hakuri, muyi ta addu’oi a masallatai da wuraren ibadu da tarurrukan addini, sannan muyi hakuri insha Allah, Allah zai dube mu da idon rahama ‘’Allah taala yace “lalle tare da tsanani akwai sauki” Sayyiduna umar yace tsanani bai taba rinjayar sauki biyu ba’. Annabi s.aw yace ‘ kuyi hakuri har sai kun iskeni a bakin tabki’ Lalle Allah yana tare da masu hakuri, kuma baya tauye ladan masu hakuri.

Allah ya kawo mana karshen‘Yan ta’adda da duk wani mai hannu a cikin wannan zalunci. Amin

JIBWIS NIGERIA.
06-Jumada Ula-1443
11-December-2021

Labarai Makamanta