Matsalar Tsaro: Izala Ta Bukaci A Mayar Da Al’amari Ga Allah

An kira yi Al’umma Musulmi da su maida dukkanin lamuransu ga Allah madaukakin sarki domin ganin an samu waraka a bangaren tsaro da ya zamewa kasanan karfen kafa.

Shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheik Abdullahi Bala Lau ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin taron da kwamitin women in Da’awah na kasa ya shirya a Yola.

Sheik Bala Lau yace komawa ga Allah madaukakin sarki shine mafita daga halin da ake ciki a yanzu don haka ya kamata Al’umma Musulmi su kasance masu sanya tsoron Allah a zukatunsa a koda yaushe da kuma gudanar da ayyukansu tsakaninsu da Allah madaukakin sarki, wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin Najeriya baki daya.

Ya kuma kirayi ‘yan Najeriya da su maida hankali wajen yin duk abinda zai kawo hadin kai da kuma cigaban kasan nan baki daya.

Sheik Bala Lau ya kuma shawarci Al’umma Musulmi musamman ma malamai da su cigaba da fadakar da Al’umma sanin muhimmanci zaman lafiya a tsakanin Al’umma baki daya.

Taron dai ya samu halarta shugabanin kwamitin women in Da’awah daga sassa daban daban dake fadin Najeriya harma da malamai daga cikin da wajen Najeriya.

Labarai Makamanta