Matsalar Tsaro: INEC Za Ta Sauya Wa Rumfunan Zabe 357 Waje A Katsina

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce za ta mayar da rumfunan zabe 357, PUs, zuwa wuraren da babu tsaro saboda kalubalen tsaro a jihar Katsina.

A cewar hukumar, ta dauki matakin ne domin bai waduk ‘yan gudun hijira, da ke jihar damar kaɗa kuri’unsu a zaben 2023.

Kwamishinan zaɓe na jihar, Farfesa Ibrahim Yahaya Makarfi ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a yau Juma’a a Katsina.

Ya bayyana cewa, dokar zabe ta 2022 ta yi tanadin tsare-tsare a bayyane da kuma bayyana yadda za a gudanar da zabe a cikin yanayi na rashin tsaro.

“Sashe na 24 na dokar zabe ta 2022 ya yi tanadi ga hukumar ta yadda na za a tauye wa wani ɗan gudun hijira ƴancinsu na zabe ba.

“Saboda haka, za mu tabbatar da cewa gwargwadon abin da ya dace, za mu bai wa duk wani wanda ya cancanci kada kuri’a damar yin amfani da ƴancinsa kamar yadda doka ta tanada.

Labarai Makamanta