Matsalar Tsaro: Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Gaggawa

Rahotanni daga Ibadan babban birnin Jihar Oyo na bayyana cewar Gwamnonin jihohi 13 a karkashin jam’iyyar PDP, a yanzu haka suna ganawa a Cibiyar Taron Kasa da Kasa na Cibiyar Kula da Noma ta IITA dake Ibadan domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro.

Gwamnonin su ne: Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato; Samuel Ortom na Benue; Douye Diri na Bayelsa; Okezie Ikpeazu na Abia da Emmanuel Udom na Akwa Ibom. Sauran sune: Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Umar Fintiri na Adamawa; Bala Mohammed na jihar Bauchi, Nyesom Wike na Ribas da Godwin Obaseki na Edo. Akwai kuma gwamna mai masaukin baki, Seyi Makinde na Jihar Oyo da Mataimakin Gwamnan Zamfara, Aliyu Gusau wanda ya wakilci Gwamna Bello Matawalle.

Ana sa ran Gwamna Darius Ishaku, na Taraba da Gwamna Ben Ayade, na Kuros Riba za su shigo yayin da taron ke ci gaba.

Gwamnonin da suka iso cibiyar taron daidai karfe 1:10 na rana a cikin motar bas sun shiga ganawar sirri. NAN ta tattaro daga wurin taron cewa taron zai mayar da hankali ne kan yanayin tsaro a kasar.

Ta kuma tattaro cewa taron wanda Shugaban gamayyar gwamnonin PDP ya jagoranta, Gwamna Aminu Tambuwal zai tattauna wasu batutuwan da suka shafi ci gaban jam’iyyar. Ana sa ran za a fitar da sanarwa bayan taro.

Labarai Makamanta