Matsalar Tsaro: El Rufa’i Ya Shiga Taron Gaggawa Da Sarakuna

@GovKaduna

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i na jagorantar wani taro kan matsalar tsaro da ta addabi jihar da sarakunan Jihar a fadar gwamnatin jihar a yau Talata.

Jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyi da malaman addinai da masu sarautar gargajiya da sauran wakilcin daga sassa daban-daban ne ke halartar taron.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, wadda ta ki ci ta ki cinyewa.

@GovKaduna

Ko a jiya sai da wasu ‘yan bindiga suka kutsa kai cikin wata makarantar Firamari suka dauki dalibai da malamansu.

Gabanin nan a ranar Asabar, sai da jami’n tsaro a jihar suka dakile wani hari da aka aki wata makaranta, inda aka kusa sace daliban makarantar sai dai harin bai yi nasara ba.

@GovKaduna

Labarai Makamanta