Matsalar Tsaro: El Rufa’i Ya Shiga Ganawar Sirri Da Jami’an Tsaro

Gwamnan jihar Kaduna Mal Nasir Ahmad El Rufa’i da mataimakiyar sa Hadiza Balarabe sun shiga ganawar sirri da babban kwamandan rundunar sojin saman Najeriya, air Mashal Isiaka Amao a fadar gwamnatin jihar Kaduna a safiyar yau laraba.

Ganawar tasu ta biyo bayan ganawar da gwamnan yayi da majalisar sarakunan jihar a jiya talata inda suka tattauna muhimman abubuwan da suka shafi tsaro.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ko a makon da ya gabata yan bindiga dauke da muggan makamai suka shiga Kwalejin gandun daji dake mando su kayi awon gaba da dalibai mata da maza. Yanzu daliban sun kwashe kwanaki 6 kenan a hannun yan bindiga ba tare da dawowa ba.

Kuma ko a jiya bayan kammala taron, an jiyo gwamnan jihar Kaduna na kara jaddada matsayar sa akan cewar babu dalilin da zai sa yayi sulhu da yan bindiga domin aikin sa a matsayin gwamna shine yasa ayi aiki da doka bawai sulhu da yan bindiga ba.

Mutane da dama a ciki da wajen jihar suna ta bada shawaran cewar durkusawa wada ba gajiyawa bane, musamman ganin yadda aka kwashi daliban nan kusan tsirara suna barci da daddare. Sannan ace za a barsu a cikin wannnan yanayi ba abu bane mai dadi.

Meye shawarar Ku ga gwamnan jihar Kaduna a halin yanzu?

Labarai Makamanta