Matsalar Tsaro: Buratai Ya Bada Magani

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanat Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya bayyana hanyoyin da za a bi don kawo karshen rashin tsaro, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka don kawo tsaro.

Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani taron tsaro da aka yi na rana guda a Arewa House dake birnin tarayya Abuja.

Ya ce a halin yanzu akwai ƙalubalen tsaro da dama a sassan kasar kamar ta’addanci a arewa maso gabas, yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, satar danyen mai da neman ballewa daga kasa a kudu maso kudu.

Buratai ya bada shawarar cewa dole a yi amfani da tsarin da kowanne dan kasa zai taka muhimmin rawa wurin magance kallubalen tsaro ta kowace fuska domin kawo karshen matsalar.

Ya yi bayanin cewa tsarin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga cikin al’umma, kamar shugabannin addini, matasa, malamai, mata, kungiyoyin al’umma, kafafen watsa labarai, da sauransu.

“Akwai bukatar a rika wayar da kan al’umma kan rawar da za su taka wurin samar da tsaro a kasar ta hanyar hukumomin kamar Ma’aikatan Wayar Da Kan Al’umma, NOA, da sauransu”.

Buratai ya kara da cewa akwai bukatar a farfado da kamfanin kera makamai na DICON don magance kallubalen rashin isasun makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi. “Wannan na da muhimmanci domin cike gibin karancin makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi da sabbin barazana.

“Don cimma hakan, Ma’aikatar Tsaro, tare da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki za su iya hada hannu don samar da kayan horaswa ga ma’aikatan DICON. “Hakan zai kara kwarewarsu da makamai da za su kera wa sojojin Najeriya”.

Labarai Makamanta