Matsalar Tsaro: Buhari Zai Wadata Jami’an Tsaro Da Manyan Makamai

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na wadata mayakan kasar da isassu kuma ingatattun kayan aiki don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro dake addabar kasar a sassa daban-daban.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana wannan kudurin yayin da yake bude babban taron manyan hafsoshin sojin kasar da kuma manyan kwamandojin sojojin daga ko’ina cikin kasar.

Yace tsaro na daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa don haka za ayi duk wani abu mai yiwuwa don inganta sashin.

Shugaban wanda Babban Hafsan rundunar Tsaron Kasar, Janaral Lucky Irabor ya wakilce shi yace yanzu haka suna magana da wasu manyan kasashen duniya kawayen Najeriya don samar da makamai masu kwari kuma ingatattu don baiwa dakarun kyakkyawan yanayin murkushe duk wani tsageranci da ta’addanci a kasar.

Labarai Makamanta