Matsalar Tsaro: Buhari Ya Ji Tsoron Gamuwarsa Da Allah – Bafarawa

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya bayyana takaicinsa kan kashe-kashen al’umma da ‘yan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da “ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah”.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da BBC Hausa kwanaki kaɗan bayan ‘yan fashin daji sun ƙona wata motar bas ɗauke da mutum kusan mutum 30 a cikinta a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.

Bafarawa ya ce: “Wajibi ne Buhari ya bi al’umma a zauna a tattauna kamar yadda ya bi su gida-gida lokacin da yake neman ƙuri’a, saboda mu taimaka masa wajen haɗuwarsa da Allah.”

Labarai Makamanta