Matsalar Tsaro Ba Ta Shafi Harkar Noma Ba – Ministan Noma

Ministan Harkokin Noma da Bunƙasa Karkara, Mahmood Abubakar ne ya bayyana hakan a Abuja, amma kuma ya ce gwamnati na ta ƙoƙarin ganin ta shawo kan tsadar kayan abincin.

Ya yi wannan bayani a gaban manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, a Shirin Mako-mako da Ministoci ke ganawa da ‘yan jaridar fadar.

Tawagar jami’an yaɗa labaran Shugaban Ƙasa ne ke shirya taron.

Farashin kayan abinci kamar shinkafa, biredi, nama da sauran su duk ya tashi, kuma a kullum ci gaba da tsada su ke yi. Yawancin kayan abinci ma farashin su ya nunka kusan sau biyu.

Sai dai ministan ya ce ba a Najeriya kaɗai ake fama da hauhawan farashin kayan abinci ba, saboda ɓarkewar annobar korona da kuma yaƙin Rasha da Ukraniya.

“Lokacin da korona ta ɓarke, ta shafi komai har da farashin kayan abinci, ga shi kuma bayan wannan har yanzu ana ci gaba da jin jiki.” Cewar Minista.

“Na yi amanna farashin shinkafa ya ɗan sauka kaɗan. Amma dai mu na nan mu na ƙoƙari a kan saisata lamarin.”

“Duk duniya ta girgiza daga ɓarkewar annobar korona da sakamakon da cutar ta kawo. Sannan kuma kai aka sake afkawa cikin wata masibar, wato yaƙin Rasha da Ukraniya. To amma dai komai zai warware, kasancewa Ma’aikatar Harkokin Noma ta na yin dukkan abin da ya zama dole da abin da ya dace wajen ganin ta shawo kan wannan tsadar kayan abinci. Ba mu yi ƙasa a guiwa ba, babu hutu babu gajiya har sai mun sauko da farashin kayan abinci a ƙasa cikin gaggawa.”

Da ya ke magana kan yadda matsalar rashin tsaro ta shafi kayan abinci kuwa, ya ce hare-haren da ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram ke kai wa cikin yankunan karkara, ya hana manoma da yawan gaske zuwa gonakin su, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Sai dai kuma ya ce duk da matsalar tsaro, “har yanzu yawan abincin da ake nomawa bai ragu can can sosai ba.”

Daga nan ya ce Najeriya na nan a kan ƙudirin ta na ganin ta kakkaɓe yunwa a faɗin ƙasar nan, nan da shekarar 2025.

Labarai Makamanta

Leave a Reply