Matsalar Tsaro: Amfani Da Sarakuna Ne Mafita – Salanken Daura

An bayyana cewar amfani da Sarakunan gargajiya shine mafita akan shawo kan matsalar tsaro wadda ta daɗe tana addabar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar, duba da yadda Sarakuna suke matsayin iyaye kuma mafi kusanci da jama’a.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mai girma Salanken Daura Alhaji Auwal Yusuf, ɗaya daga cikin ‘yan Majalisar Masarautar Daura kuma mai bada shawara ta musamman ga mai Martaba Sarkin Daura, a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

Salanken Daura ya cigaba da cewar a fili yake Sarakuna ne kaɗai za su iya ɗaukar ragamar gano bakin zaren matsalar da ke addabar Arewa saɓanin ‘yan Siyasa da ake amfani da su.

Ya kuma yaba da matakin da sanannen malamin nan na garin Kaduna Dr. Ahmad Gumi ya ɗauka na shiga cikin dazuka domin ganawa da’yan Bindiga, da kuma shawarar da Malamin ya bayar na cewar a yi zaman sulhu da ‘yan Bindigar a matsayin wata hanya ta samun nasarar.

Hakazalika Salanken Daura ya kuma yi tsokaci akan kalaman gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i na cewar babu amfanin sulhu da ‘yan ta’adda illa ayi amfani da ƙarfi a murkushe su, inda ya ja hankalin gwamnan akan muhimmancin sulhu, domin a tarihin duniya an sha samun inda rikici da fitintinu suka yi ƙamari a tsakanin ƙasashe amma a ƙarshe teburin sulhu aka hau kuma aka yi nasara.

Basaraken na Daura ya kuma yi kira da babbar murya ga jama’ar Arewa da su cigaba da zama lafiya da sauran jama’ar kasar, duk da rikicin da ke faruwa yanzu haka a sashin Kudancin kasar musamman a yankunan Jihohin Yarbawa na rikici da Fulani, inda ya bayyana rikicin a matsayin wani shiri ne da aka ƙirƙira da niyyar mayar da hannun agogo baya akan nasarorin da gwamnatin Buhari ke samu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply