Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Matsalar Tsaro: Aisha Buhari Ta Nemi Afuwar ‘Yan Najeriya

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta ba ‘yan Najeriya hakuri kan rashin tsaro da tsadar rayuwa da ya jefa ‘yan kasar cikin rayuwar kunci a shekaru bakwai da suka shude.

Ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin addu’a da lakca ta musamman don bikin ranar samun yancin kai karo na 62 da aka yi a masallacin kasa a Abuja,

A cewar ta, rage darajar naira da cigaba da faduwar darajar naira a kasuwannin canji ya shafi tattalin arziki wacce ta ce ya yi sanadin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta wurin ilimi, lafiya da harkokin yau da kulum. Duk da haka ta yaba wa kokarin dakarun sojoji wurin magance ƙalubalen tsaro a kasar kuma ta musu fatan alheri.

“Kamar yadda kuka sani, wannan gwamnatin tana daf da zuwa karshen wa’adinta kuma wanna shine bikin ‘yancin kai na karshe da za ta yi, ina addu’ar mu yi zabe lafiya da mika mulki. “Ba dole ne gwamnatin ta zama ba ta da nakasu ba, amma ina son yin amfani da wannan damar in nemi yafiya daga wajen malamai da ‘yan Najeriya baki daya.

“Na yi murnar gani cewa jami’an tsaron mu sun tashi suna tunkarar ƙalubale fiye da kowane lokaci. A yanzu suna kokarin kawo karshen yan bindiga, masu garkuwa da sauran bata gari. Ina jinjinawa kokarin jami’an tsaron mu kuma ina addu’a Allah ya kara musu nasara.”

Exit mobile version