Matsalar Tsaro: Addu’a Ce Mafita – Etsu Nupe

Daga: Muhammad Sani Yusuf Nassarawa.

Mai Martaba Etsu Nupe Dr.Yahaya Abubakar ya bukaci Al’ummar Nijeriya su dage da Addu’a Musamman a wannan Lokaci da muke Ciki Ganin yadda Rashin Tsaro ya yi Kamari a Kasarnan.

Sarkin yace Babu wani abinda ya dace da Jama’a a daidai wannan Lokaci face addu’a ganin yadda Rashin Zaman Lafiya da Satar Mutane don Karbar Kudin Fansa da Sauran Fitintunu Sukayi Katutu a sassa Daban-Daban Dake Kasarnan.

Sarkin yayi Wadannan kalamaine Alokacin da yake Zantawa da Tashar Yanci a Abuja.

Ya Kara da Cewa Zaman Lafiyar Kasarnan shine abinda Zai kawo ci gaban ta, Kama daga mutunta addinan juna da kaucewa abinda Zai kawo Rabuwar Kai.

Da yake Magana akan Zaben Shekara ta 2023 Mai Tafe Mai Martaba Sarkin, ya bayyana yin Katin Zabe a Matsayin makamin da Al’umma za suyi amfani da shi Domin Zabar Shugabanni na gari Wadanda za su ciyar da Kasarnan gaba.

Daga Karshe Kara jadda bukatar Dake akwai Wajen Gwamnati ta Kara Himma don Kawo Karshen Matsalar Tsaro a Kasarnan.

Labarai Makamanta