Matsalar Tsaro: A Daina Ɗora Laifi Akan Gwamnatin Tarayya Kaɗai – Ministan Tsaro

Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin Jihohi da sauran wakilai da su ba da tasu gudummawar wajen magance ‘yan Bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar, ba wai ɗora laifi akan Gwamnatin Tarayya kaɗai ba.

Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya ya yi wannan furucin a ranar Asabar a Kano bayan ya sake jaddada rajistarsa na jam’iyyar APC a shiyyarsa ta Galadanchi da ke ƙaramar hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Da yake amsa tambaya kan matsayar da gwamnatin tarayya ke da ita a kan ‘yan ta’adda yayin musayar ra’ayi tsakanin wasu gwamnoni, Ministan ya ce gwamnatin tarayya na nan kan bakanta na kare rayuka da dukiyoyi.

“Ba za mu iya zama mu ba mutane damar yin magana yadda suke so ba. Ya kamata suyiwa mutanensu aikin da wajaba akansu.

Ya kamata duka gwamnoni suyi aikin kansu. Suna da abubuwa da yawa da zasu iya yi don dakatar da wannan ta’addancin da sauran al’amuran tsaro.

“Amma kukan cewa ya kamata mu aikata hakan ko kuma kada mu aikata hakan ba zai magance matsalar ba. “Kowa ya koma wurin mutanensa.

Kowa, ina nufin, duk masu rike da mukaman siyasa su koma yankunansu su ga abin da ke faruwa a can.

Akwai talauci, akwai sakaci, babu makaranta, babu cibiyoyin kiwon lafiya, babu komai! “Don haka, idan za su iya mai da hankali kan hakan shi kadai, ina ganin kasar za ta kubuta,” in ji shi.

Labarai Makamanta