Matsalar Mai: NNPC Ya Bada Umarnin Jigilar Mai Ba Dare Ba Rana

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu akwai wadataccen mai a faɗin Najeriya.

Kamfanin na NNPC, ya ce ya bayar da umarnin jigilar mai daga manyan rumbuna da kuma sayar da shi a gidajen mai a fadin kasar, ba dare ba rana a kokarin kawo karshen matsalar man da ake ciki a yanzu.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Talatar nan 15 ga watan Fabrairu 2022, ya ce yana ba wa ‘yan kasar tabbacin daukar matakan da suka dace domin hanzarta samar da man a fadin kasar.

Sanarwar ta ce manyan kamfanonin mai da dukkanin masu harkar sayar da man suma sun kama aiki ba dare ba rana domin wadata ko’ina.

Kamfanin ya shawarci jama’a da su daina tururuwar sayen man saboda fargabar karancinsa, domin a cewarsa yana da sama da lita biliyan daya ta man, domin amfanin ababan hawa da manyan injina.

Sanarwar ta ce masu sanya ido na kamfanin da hadin guiwar jami’an tsaro sun dukufa aiki don tabbatar da raba man a fadin kasar.

Bugu da kari sanarwar ta ce a kokarin da kamfanin yake na tanadar da wadataccen mai a kasar, ya tsara adana man lita biliyan 2.3 daga yanzu zuwa karshen watan nan na Fabrairu, wanda hakan zai sa a samu man wadatacce fiye da na kwana 30, da ake tanada ko da an shiga karanci.

An shiga matsalar man a Najeriya tun kusan mako biyu da ya gabata sakamakon gurbataccen mai da aka shigar da shi kasar, wanda ya haddasa lalacewar ababan hawan jama’a.

Labarai Makamanta