Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Matsalar Mai: Majalisa Ta Ba NNPC Wa’adin Mako Guda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci kamfanin mai na kasa NNPC ya kawo karshen karancin fetur da ake fama da shi a cikin cikin mako guda.

A cewar majalisa tsawon watanni ‘yan Najeriya na wahalar fetur wanda ke tasiri ga tattali arzikin kasa da jefa al’umma cikin wahala.

Sannan kamfanin na bijiro da wasu dalilai a matsayin hujjar wahalhalun mai a fadin Najeriya, don haka wanna gargadi ne ga NNPC.

Umarnin majalisa na zuwa ne bayan a karshen mako hukumar DSS ta bai wa NNPC da kungiyar IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su wadatar da mai a fadin Najeriya.

Tun farkon shekara ta 2022 kusan baa shafe wani lokaci mai tsawo ba tare da ‘yan Najeriya sun shiga wahalar fetur ba.

Ana danganta wannan dalili da nayin farashin dala da kuma rikicin Rasha da Ukraine.

Exit mobile version