Matsalar Mai: DSS Ta Ba NNPC Wa’adin Awa 48

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bai wa kamfanin man NNPC da kungiyar dalilan man fetur ta IPMAN wa’adin sa’o’i 48 su tabbatar da wadatuwar fetur a fadin kasar.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, ne ya fitar da sanarwar a Abuja bayan ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin fetur.

Sanarwar ta ce NNPC ta tabbatar da cewa tana da wadataccen fetur jibge da zai wadatar da ‘yan kasar har bayan bukukuwa karshen shekara.

Ya ce an baza jami’an DSS a kowanne kusurwa na kasar domin hukunta duk maso boye mai ko yiwa harkar samar da mai zagon-kasa.

Sanarwar ta ce irin wannan matsala na fetur da ake haifarwa a kasar na taka rawa wajen sake asasa matsalolin tsaro.

Labarai Makamanta