Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ɗan takarar zama shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai kawo karshen yawan shiga yajin aikin kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) idan ya haye karagar mulki.
Tsohon gwamnan jihar Legas din ya dauki wadan nan alkawurran ne a wurin gangamin yakin neman zaben APC wanda ya gudana a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Dan takarar ya sha alwashin daidaita bangaren ilimi a Najeriya domin kowa ya samu damar karatu cikin walwala da kuma natsuwa.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa zai samarwa manoma da kayayyaki da tallafin noma kuma idan har ya yi nasara zai maida arewa maso gabas ta zama shiyyar fitar da kayayyaki.
“Zan fadada wuraren ba da rancen kudi ga ɗaliban jami’o’in Najeriya. Zan tabbata tsarin neman ilimi musamman a jami’o’in ya daidaita ta hanyar magance yawan shiga yajin aikin ASUU.” “Ba za’a sake samun damuwar shiga yajin ASUU ba a jami’o’in mu idan na zama shugaban kasa.”
You must log in to post a comment.