Matawalle Zai Rasa Kujerar Gwamna Muddin Ya Koma APC – Yari

Tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari ya shaida wa gwamna Bello Matawalle cewa zai rasa kujerarsa muddin ya bar jam’iyyar PDP, bisa shari’ar kotun koli da ta bashi nasarar samun mulkin a 2019.

Yari ya shaida hakan ne a ofishin jam’iyyar APC da ke birnin Gusau a jiya Lahadi lokacin rabon kayan abincin ramadan ga magoya bayan APC a cewar Jaridar Punch ta Najeriya.

Tsohon gwamnan wanda Sanata Kabiru Marafa ya wakilta na cewa babu wani mutum da ya sanar da su ta baka ko a rubuce cewa Matawalle ya koma APC.

Ya kuma yi gargaɗin cewa tunda kotun koli ta soke nasarar APC da sanar da PDP a matsayin wacce ta yi nasara kuma dole ta ci gaba da mulki har 2023.

Labarai Makamanta