Matasan Kudancin Kaduna Sun Lashi Takobin Ganin Bayan ‘Yan Bindiga

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Matasan Kudancin Jihar sun sha alwashin cewa ba zasu sake naɗe hannu suna kallo yan bindiga na kai hari yankunasu, suna sace mutane ba.

Matasan sun gargaɗi yan bindigan ne karkashin kungiyar mutanen kudancin Kaduna (SOKAPU) bangaren matasa, a wata sanarwa da suka fitar cikin fushi.

A sanarwar da shugaban matasan SOKAPU na ƙasa, Kwamaret John Isaac, ya fitar, Matasan sun yi kira ga mutanen dake zaune a yankin kudancin Kaduna su tashi tsaye su daina jiran kowa, su kare kansu daga sharrin waɗannan mutanen.

“Wajibi mu tashi tsaye domin kare kan mu daga sharrin yan ta’addan nan, waɗan da suka samu mafaka a dazukan mu, suna kisanmu da yin garkuwa da mutanen mu gami da yin fyade ga matanmu”

Matasan sun kuma bayyana rashin jin daɗinsu da dana sani kan harin da yan ta’addan suka kai, inda suka kashe mutum kuma suka tasa keyar wasu 50 a Ungwan Gimbiya, Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun.

Kazalika matasan sun bayyana cewa a watan Yuli, wasu maharan sun farmaki waɗan nan yankuna inda suka yi mummunan ta’adi na kisa da fyade.

“A harin watan Yuli, an kashe mana mutune kuma mun biya miliyoyin kudi a matsayin fansa.” “A kwanan nan kuma sun kashe wasu mutunen sun sace wasu adadi mai yawa a Ungwan Gimbiya, Sabon Tasha, kuma garin yana cikin birnin Kaduna.”

Matasan SOKAPU sun kara da cewa abun da takaici yadda yan ta’adda ke ɗai-ɗaita kauyuka, kuma ya zama wajibi abun ya zo ƙarshe.

Labarai Makamanta