Matasan Arewa Sun Yi Tir Da Masu Alakanta Pantami Da Ta’addanci

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a garin Kaduna, Shugaban Ƙungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa, yace ba abu bane wanda za’a lamunta yadda wasu ke amfani da siyasa wajen alakanta ministan sadarwa Pantami da ayyukan ta’addanci.

Kamal Funtuwa ya kara da cewar ba wani abu bane ya sanya masu adawa da Pantami suka cigaba da kunno mishi wuta akan zargin ta’addanci, sai dai kawai kasancewar shi malamin addinin Musulunci, inda ya bada misali da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda yake matsayin Pastor a addinin Kirista, amma babu wani Musulmi da ya yi korafi, to bisa wane dalili za’a taso Pantami gaba? Inji shi.

Matasan na Arewa sun koka dangane da yadda jama’a a Najeriya suke barin jaki su koma dukan taiki, inda suka bada misali da yadda kwanan nan majalisar kasa ta amincewa Buhari ya amso tarin Basussuka wadanda basu da wani amfani ga ƙasar, amma babu wanda ya fito ya yi ƙorafi akan hakan, sai batun Pantami ake ta surutu akai.

Daga karshe matasan na Arewa sun ce ko kaɗan ba za su lamunci duk wani yunkuri na kokarin haddasa rikicin addini a ƙasar ba.
“Muna goyon bayan minista Pantami akan ƙoƙarin da yake yi na inganta tsaro da yakar ta’addanci da yake yi a Ma’aikatar shi, sannan muna yin tir da dukkanin masu kokarin haifar da ruɗani cikin lamarin.

Labarai Makamanta