Matasa Sun Roki Sarkin Bauchi Ya Daidaita Da Dogara

Daga Adamu Shehu Bauchi

Matasa Yan-rajin Kare muradin Tsohon kakakin majalisar tarayya Yakubu Dogara sun roki mai martaba Sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu da ya sake duba wan nan dakatarwa da masarautar Bauchi tayi masa a dalilin cewa bai zo ya jajantama al’umman Jihar ba bayan rikicin Bogoro da ya faru a kwanan baya ba.

Matasan sunyi wan nan rokon ne a lokacin da suke nuna alhinin su ma manema labarai kan wan nan batu a sakatariyar yan-jarida reshen jihar Bauchi,

Shugaban Kungiyar Garba Usman Kirfi, yace sunzo me su gaya ma duniya irin abubuwan da suke faruwa a Jihar Bauchi basu rasa nasaba da siyasa, Kuma hakan ba daidai bane, jawabin nasa dai yana mayar da martani ne kan hukuncin da masarautar Bauchi ta dauka a kan tsohon kakakin majalisar tarayya, a jiya na dakatar da shi daga sarautar Jakadan Bauchi a majalisar Sarkin.

Yace suna fatan za’a sasanta domin cewa shi Yakuba Dogara baya son tashin hankali, mutum ne mai son zaman lafiya, “dalilin da yasa Yakubu Dogara baizo ba Yana gudun kar a sake hatsaniya ko turmusi da wani tashin hankali na dabam”.

“Don haka ne kawai bawai don ya raina masarautar Bauchi bane ko Mai martaba sai don samarvda zaman lafiya a tsakanin al’ummar Jihar Bauchi” ya fada.

Indai ba a manta ba a jiya ne ranar Talata 23 ga watan daya na shekara dubu biyu da ashirin da uku 2023 Masarautar Bauchi ta fitar da sanarwar dakatar da tsohon kakakin majalisar tarayya Yakubu Dogara a mukaminsa na Jakadan Bauchi bisa zargin yana ma masarautar karan tsaye, da kuma rashin mutun tawa.

Sanarwar dai wanda Galadiman Bauchi Suveyo Ibrahim Sa’idu Jahun ya fitar Kuma ya rabawa manema labarai tare da sa hannun hadimin Masarautar Bauchi.

Har- ila yau sanarwar dakatarwa tayi nuni da cewa wan nan hukunci da suka dauka nan take sai har illa masha Allahu ne.

Labarai Makamanta