Matan Gwamnoni Sun Yi Kiran Samun Daidaito A Rigakafin CORONA

Ƙungiyar matan gwamnonin ƙasar nan sun yi kira ga gwamnatin tarayya akan samar da daidaito da guje wa nuna fifuko sannan kada su mance da yin haka wajen rarraba rigakafin cutar corona da ta shigo Najeriya.

Kungiyar matan gwamnonin 36 ta yi wannan kira ne a wani saƙo da ta fidda dan tunawa da ranar mata ta duniya ran litinin a birnin tarayya Abuja.

Saƙon ya ƙunshi sa hannun Shugabar kungiyar, Erelu Bisi Fayemi, da shugabar kungiyar matan gwamnonin arewa, Dr Amina Abubakar Bello, da kuma shugabar matan gwamnonin kudu, Mrs Betsy Obaseki.

Matan gwamnonin sun ce yakamata ace suma anyi musu rigakafin don su nuna wa mutane ingancinshi, kamar yadda tuni aka fara yi wa Maza allurar.

“Duk da muna farfaɗowa daga wannan cutar da muka tsinci kanmu a ciki, muna kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da daidaito wajen samun rigakafin.” a cewar matan.

Matan Gwamnonin sun ƙara da cewa: “Muna kira ga mata da su amince a musu allurar rigakafin da zaran damar hakan ta samu, mu kan mu za’ayi mana don mu tabbatar muku cewa rigakafin mai inganci ce.”

Ƙungiyar matan sun kara yin kira da abar mata su fito a dama dasu a fannin shugabanci, domin akwai matsaloli dayawa da mata zasu iya warwarewa. “Muna da kwarin gwuiwar cewa, idan aka ƙarfafa mata suka zama shugabanni, to za’a samu hanyoyi da dama wajen warware matsalolin da muke fuskanta a ƙasar.

” A matsayin mu na matan gwamnoni zamu cigaba da ba mazan mu goyon baya kuma zamu tuna musu haƙƙin dake kansu na samar da tsaro, kare rayukan al’umma da kuma samar da ayyukan yi musamman ga mata”. A wani labarin kuma Jam’iyar APC tayi Allah wadai da kashe-kashen da akeyi a jihar Ekiti A sanarwar da jami’in yaɗa labarai na jam’iyar ya fitar ya yi Allah wadai da kisan wasu manoma biyu da akayi kwanan nan a yankin Isaba Bayan haka ja/

Labarai Makamanta