Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai bar birnin Abuja a yau don zuwa kasar Vitenam, inda zai gana da shugaban kasar; Nguyn Xuân Phúc, mataimakins; Mr. Pho Chu Tich Nuroc da sauran jiga-jigan kasar.
Ziyarar ta Osinbajo a kasar ta Vietnam za ta kara dankon kasuwanci da zumunci tsakanin Najeriya da kasar, Idan baku manta ba, a kokarin kulla alakar kasuwanci da kawance, firayinminsitan kasar, Vuong Hue ya kawo ziyara Najeriya, inda ya gana da Osinbajo a 2019.
Duk da cewa Najeriya da Vietnam na da alaka mai zurfi tun 1976 ta diflomasiyya, Osinbajo ne shugaba a Najeriya na biyu da ya kai ziyara aiki zuwa kasar bayan tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
A wannan ziyarar, Osinbajo zai halarci wani zama da Zauren kasuwanci na Vietnam, inda hakan zai taimaka wajen hada alaka tsakanin ‘yan kasuwan Najeriya da na kasar. Tare da damammaki masu yawa a fannin noma da fasaha tsakanin Najeriya da Vietnam, tattaunawar da Osinbajo zai halarta za ta mai da hankali ne ga zurfafa alakar kasashen biyu a fannonin kasuwanci. Rahoto ya bayyana cewa, Osinbajo zai kammala ziyarar aikin ne a ranar Laraba.
You must log in to post a comment.