Mata Na Da Gagarumar Rawar Takawa Wajen Samar Da Tsaro – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna goyon bayansa kan kudirin matan shugabannin kasashen Afirka, AFLPM, wanda zai maida hankali kan tabbatar da zaman lafiya da kawo cigaba a nahiyar.

Da yake jawabi a wurin buɗe taron karo na 9, Buhari ya roki shugabannin kasashen Afirka da masu ruwa da tsaki su tallafa wa matan wajen gina al’umma masu zaman lafiya.

Shugaban ƙasan ya nuna damuwarsa kan yadda zaman lafiya ya kubce kuma ya jawo nakasu a ɓangaren cigaba na kasashen Afirka da dama.

“Ayyukan yan ta’adda da yan fashin daji ya jawo mutane da dama sun bar gidajensu, kuma ya jefa wasu cikin kangin talauci.” “Babu tantama mata da kananan yara ne wannan matsalar ta fi yiwa illa.

Saboda haka a matsayin ku na iyaye mata, na yi imanin cewa kuna da rawar da zaku taka wajen sake gina zaman lafiya.” “Naji daɗin sanin cewa kungiyar ku tana aiki ba dare ba rana wajen samar da ingantaccen zaman lafiya a kasashen mu na Afirka ta hanyoyi daban-daban.”

Buhari ya yaba wa matarsa, Dakta Aisha Buhari, bisa kokarin da ta yi na samun wuri a madadin sauran matan shugabannin Afirka domin gina sakatariyar su a Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply