Mata Da Matasa Ne Suka Zugani Fitowa Takarar Shugabancin Kasa – Bello

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya fito ya tabbatar da cewa babu shakka ya na da niyyar neman kujerar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa na 2023, kuma hakan ya biyo bayan kiraye kirayen da ya rinƙa samu a sassa daban daban na kasar ana buƙatar bada tashi gudummuwar.

Gwamnan ya na wannan bayani lokaci mai tsawo bayan wa’adin da wasu kungiyoyin matasan kasar nan su ka ba shi ya shude. Da yake magana da ‘yan jarida a garin Abuja, Alhaji Yahaya Bello ya ce ba zai yi garaje ba, zai jira har lokacin da za a buga gangar siyasa kafin ya shiga takarar.

“Ba na daukar wannan a matsayin takarata. Takara ce ta matasa, masu taso wa, mata, marasa galihu, marasa karfi da wadanda ake danne wa a al’umma.”

“Wadannan su ne mutanen da ke kiran in zo in bauta wa kasa, in fito neman takarar shugaban kasa a zaben 2023. Saboda gudun saba doka, zan jira sai lokaci ya yi.”

“Kuma magana ta gaskiya ita ce a cikinsu na fito, gidan masu karamin karfi, kuma ga ni matashi.” Yahaya Bello ya ce marasa hali da masu karamin karfi da wadanda ake zalunta sun taso shi gaba a kan ya yi takarar, don haka yake ganin ba zai iya ba su kunya ba.

Gwamnan ya sake yin fatali da kiran da ake yi na cewa ya kamata mulki ya koma Kudu, ya ce babu wata yarjejeniya ta kama-kama a tsarin mulkin jam’iyyar APC.

“Na yi imani cewa matasa su na da lakanin da za su iya gyara kasar nan, maganar matasa ake yi, ba batun Kudu, Arewa ko wane Musulmi ne ko Kirista ba.” Inji Bello.

Wasu su na ta ba gwamnan shawarar ya nemi kujerar shugaban kasa a 2023, kuma tun tuni fastocin takarar Yahaya Bello su ka fara yawo a wasu jihohin Najeriya. Kwanaki har an ji yadda wata kungiyar magoya bayan Yahaya Bello mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutanen Najeriya da su marawa gwamnan baya a 2023. Wannan kungiya ta bukaci mutane su tabbatar cewa Bello ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Labarai Makamanta