Masu Kiran Gwamnati Ta Kamani Kidahumai Ne – Dr.Gumi

Shahararren Malamin addinin Muslunci nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya soki lamirin dukkanin masu kira ga gwamnati ta kamashi saboda ganawar da yake yi da yan bindiga, domin samun maslaha.

Dr. Gumi ya siffanta masu hakan a matsayin kidahumai saboda ya kamata su san cewa tare da jami’an gwamnati suke zuwa ganawar da ‘yan bindigan ba wai gaban kanshi yake yi ba.

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a gidansa dake Kaduna, inda ya kara da cewa ba shi bane mutumin farko da ya fara tattaunawa da yan bindiga. Yace, “Ko gwamnan jihar Kaduna ya zauna da su, gwamnan Zamfara ya zauna da su.”

“Ba ni bane mutumin farko da ya fara tattaunawa da su ba. Ni kawai na kara nawa ne, kuma na gansu a matsayin mutane masu son addini; addini kadai ke koyar da cewa jini na da daraja.”

“Ina kokarin tattara su ne in koyar da su darajar rayuwa. Ban taba ziyartar yan bindiga ba tare da wani jami’in gwamnati ba.” “Dukkan ‘yan bindigan da muka gana da su tare da jami’an gwamnati ne, shi yasa nike kiran masu cewa a kamani kidahumai.”

Dr. Gumi ya kara da cewa sulhu da ‘yan bindigan na haifar da ‘da mai ido. “Tattaunawa da su ya kawo sakamako cikin sauri. Idan kana tattaunawa da mutumin da yayi zurfi cikin aikata laifi, idan ka je masa matsayin dan sanda, za ka samu matsala amma idan kaje masa matsayin Fasto, zai fada maka laifukan da yake aikatawa,”.

“Saboda haka muna zuwa musu a matsayin malamai, sai su samu kwanciyar hankali su bayyana mana matsalolinsu. Mu kuma sai muka yadda zamu kwantar musu da hankali.” “Ka san ko wani mutum na da addinin da yayi imani da shi, dalilin da yasa muke haka kenan,” Ya kara.

Labarai Makamanta