Masu Hannu Da Shuni Na Da Hannu A Tabarbarewar Tsaro – Al-Mustapha

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Manjo Hamza Al- Mustapha wanda ya taba zama jami’in da ke kula da tsaron Janar Sani Abacha, ya yi magana game da sha’anin rashin tsaro a Najeriya dama Duniya baki ɗaya.

An ruwaito Manjo Hamza Al- Mustapha yana zargin masu kudi da hannu a matsalar tsaron da ya addabi jihohi da dama yanzu a Najeriya. Hamza Al-Mustapha yace attajiran da su ke iya mallakar manyan makamai da miyagun kwayoyi ne ummul-haba’isin halin da al’umma suka shiga ciki a yau.

Da yake zantawa da manema labarai a gidan rediyon VOA, Manjo Al- Mustapha ya bayyana cewa akwai bukatar masu kishin kasa su hada-kai, su ceto Najeriya. Tsohon sojan yace dole sai masu mulki sun tashi tsaye domin a magance matsalar da ake ciki saboda akwai wadanda ke kashe kudi domin kawo tarzoma.

“Lokaci ya yi da duk wani mai kishin Najeriya, mai son kasar nan ko Afrika ko Duniya a ransa, ya tashi-tsaye, ya bada gudumuwarsa. “Abubuwa ba su tafiya yadda suka kamata ba.

Akwai mutanen da suke kashe kudinsu domin su tada zaune-tsaye, da alama su na yin nasara.” “Yadda suke da makamai yanzu a Afrika, da kuma kwayoyi iri-iri da mutanen da suke amfani da su, sun fara neman karbe iko a kasashe.”

Labarai Makamanta