Masu Hanƙoron Ɓallewa Daga Najeriya Jahilai Ne – Osinbajo

An bayyana waɗanda suke hanƙoron ɓallewa daga Najeriya da zimmar samar da wasu ƙasashen a cikin Najeriya da cewar Jahilai ne kuma wawaye wadanda ke da ƙarancin tunanin rayuwa.

Mataimakin Shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wannan furuci, lokacin da yake tsokaci akan shelanta ballewa daga Najeriya da wasu tsageru daga yankin kudu maso yamma da Kudu maso gabashin kasar nan suka yi.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci masu kira ga raba Najeriya da su sake tunani, ya kara da cewa idan Najeriya ta wargaje, dole su bukaci katin biza domin tafiya sassan arewa kamar Kano.

Osinbajo ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron tattaunawa na 12 na bikin cika shekaru 69 na Bola Tinubu da aka gudanar a jihar Kano.

Mataimakin Shugaban kasar, wanda shine babban bako na musamman, ya ce taron a farko an shirya gudanar dashi ne ta yanar gizo, amma Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya dauki nauyin taron a zahiri wanda kuma zai gudana ta manhajar Zoom.

“Ga masu son ballewa zuwa kananan abubuwa, zuwa kananan kasashe, ya kamata a tuna musu cewa da ba za mu iya karbar tayin Gwamna Ganduje na zuwa Kano a takaitaccen lokaci ba tunda duk da za mu bukaci Visa don zuwa Kano,” in ji Osinbajo.

Osinbajo ya kara da cewa Kano waje ne mai matukar muhimmanci domin nan ne gidan masu akida ta ci gaban kasa.

Labarai Makamanta