Masu Fyade Na Samun Kariya Wajen Shugabanni Ne – Ummi El Rufa’i

Uwargidan Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Aisha Unmi Elrufai ta yi kira ga Sarakunan Gargajiya da sauran shugabannin al’umma da suka tona asirin masu aikata laifin fyade kuma su daina ba su kariya a yayin da aka kama mutum da laifin fyade. Ta ce lokaci ya yi da za a kawo karshen binne abinda ya shafi laifin fyade.

Uwargidan Gwamnan ta bayyana hakan ne a yayin da jagoranci tawagar yaki da fyade a jihar Kaduna (KASAS) domin shawo kan matsalar fyade da sauran al’amuran da suka shafi cin zarafin jinsi da ta fita a yau Juma’a a yankin Turukun dake karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna.

Ta kara da cewa matsalolin fyade musamman ga kananan yara masu karancin shekaru na kara ta’azzara a fadin jihar Kaduna, kuma lamarin na kara kamari ne saboda masu aikata laifukan suna samun kariya daga wurin shugabannin al’umma.

A yayin da take yi wa shugabannin al’umma jawabi wadanda suka hada da Sarakunan gargajiya, shugabannin addini da sauransu, Uwargidan gwamnan ta bayyana cewa “mun zo nan ne domin ci gaba da yaki kan lamarin fyade domin ganawa da ku shugabannin al’umma, sarakunan gargajya, shugabannin addini, kungiyoyi, matasa da sauransu domin taya mu yaki da wannan matsala. Mun zo nan ne domin samar da hanyoyin da rahotannin fyade za su dinga isowa gare mu. Muna so ku taya mu yakar matsalar ta hanyar zama hukuma a yakinka.

“Ba mu baku goyon bayan ku daki wanda aka kama da laifin fyade ba, abinda ake bukata shine ku taimaka ku kama shi domin mika shi ga hukuma.

“Mun samu labarin cewa shugabannin al’umma da kan su suke bada kariya ga masu aikata fyade. Don haka muna kira da ku daina hakan. Saboda idan muka ci gaba da yi wa masu aikata fyade afuwa saboda makobtan mu ne, ko ‘yan uwanmu ne, ko kuma saboda muna so mu rufawa wadda aka yi wa fyade asiri don ta samu wanda zai aure ta a gaba, to masu aikata fyade za su ci gaba da aikatawa tunda sun san cewa ana yi musu afuwa”.

A yayin da yake mayar da martani a madadin shugabannin al’ummar, Dagacin Kauyen Turukun Sabuwa, Alhaji Ibrahim Usman ya yaba da yadda matar Gwamnan ta zabi yankin nasu a matsayin gari na farko da aka soma gabatar da shirin yaki da fyaden

Ya kara da cewa kasancewar garin Turukun shine mahaifar Sarauniya Amina, za su jagoranci yaki da mataalar fyade da sauran laifuka na cin zarafin jinsi.

Labarai Makamanta