Masu Fatan Raba Najeriya Za Su Ji Kunya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin koli na harkokin addinin musulunci, NSCIA, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce ba za a yi yaki ba a Nijeriya duk da kiraye-kirayen rabuwa da wasu sassan kasar ke yi, kuma tabbas masu wannan fata za suji kunya.

Sarkin Musulmin ya furta hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja yayin taron Kwamitin Addinai na Kasa, NIREC, da ake yi sau hudu a kowanne shekara.

Sarkin Musulmin ya ce ya yi imani da sulhu kamar yadda addinin musulunci ya koyar da shi kuma zai yi amfani da sulhun domin samar da zaman lafiya. “Mutane suna ta maganan yaki, ba za a yi yaki a Nijeriya ba, waye zai yi yaki da wa? “A gida daya, muna samun musulmi da kirista, akwai kabilu a kasarku, kunyi auratayya tsakanin ku. “Don haka, duk hayaniyar da mutane ke yi kawai ne domin su samu wani abu a kasar, idan ka dube su, tsiraru ne.

“A kasar nan, akwai mutane nagari da suke nufin talaka da alheri da sauran mutane kuma wannan shine abin da Allah ya hallice mu mu aikata,” in ji Sultan.

Ya kara da cewa, “Don haka mu cigaba da aiki tare, mu cigaba da zama tare, mu cigaba da tattaunawa, Na yi imani da sulhu kuma babu abin da zai canja min zuciya ta domin addini na ya koyar da sulhu kuma na yi imanin cewa babu abin da ya fi karfin a warware shi domin ko yaki ana yi ne domin a samar da zaman lafiya.

“Amma idan ka san za ka samar da zaman lafiya ba tare da yaki ba, mai zai saka ka dauki makamai? Zaman lafiya shine abu mafi muhimmanci .”

Labarai Makamanta