Masu Cuwa-Cuwa A Daukar Ma’aikata Za Su Gamu Da Fushina – Buhari

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin gwamnatinsa za ta hukunta duk jami’in da aka samu da daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba, da ma’aikatan boge da cushen albashin ma’aikata.

Shugaban ya yi kalaman ne a ranar Talata, lokacin da ya bude babban taro karo na uku kan yaki da rashawa a ma’aikatun gwamnati da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ke shiryawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar yaki da rashawa ta kasar ICPC, ta yi bayani a kan yawan kudaden da gwamnati ke batarwa, da karuwar daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba, da karin albashin babu gaira bare dalili da wasu ma’aikatun gwamnati ke yi ga ma’aikatan da a zahiri babu su.

Da kudaden da ake kashewa na tafiye-tafiye a ciki da wajen Najeriya, da karuwar bukatun ‘yan siyasa da aka nada mambobin wasu kwamitoci, ba tare da bincikar inda aka kwana kan hakan ba, sai uwa uba danbarwar cushe a kasafin kudi da sauransu.

Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba, za kuma ta hukunta duk wanda aka samu da laifin aikata hakan.

‘‘Mun rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa ta hanyar cika alkawarin da muka dauka na karasa ayyukan da sauran gwamnatocin da suka gabata sukai watsi da su, da tabbatar da ma’aikatu ba su yi shelar sabbin ayyuka ba har sai an kammala wadanda ke kasa,” in ji Buhari

Labarai Makamanta