Masu Adawa Da Takarata Za Su Mutu Da Bakin Ciki – Gwamnan Babban Banki

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan babban bankin ƙasa (CBN) Godwin Emefiele ya ce yana jin dadin duk wani wasan kwaikwayon da ke zagaye da burinsa na takara a 2023, kuma yana da tabbacin masu adawa dashi za su kunyata.

Emefiele ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi game da martaninsa kan rahoton cewa shugaban kasar ya bukaci ya yi murabus bayan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa Emefiele ya ce: “Babu labari a yanzu, amma za a samu labari a nan gaba. Kun ji ni, na ce ba labari yanzu amma za a samu labari nan kusa.”

Amma da aka bayyana masa cewa, ’yan Najeriya sun damu da matsayinsa, sai ya ce: “Ku bar su su kamu da ciwon zuciya. Yana da kyau a kamu da ciwon zuciya. Ina jin dadi hakan sosai.”

Gwamnan babban bankin dai na fuskantar matsin lamba tun bayan da ya sayi fom din tsayawa takara na jam’iyyar APC mai mulki, lamarin da ya harzuka da dama inda wasu ke kiransa da ya sauka daga mulki.

Labarai Makamanta