Masarautar Daura Ta Tabbatar Wa Amaechi Da Sarautar Dan Amanar Daura

Rahotanni daga masarauratar Daura dake jihar Katsina na bayyana cewar mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar ya ce ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya cancanci sarauta a Daura wannan ya sanya aka nada shi sarautar Ɗan Amanar Daura.

Galadiman Daura kuma Hakimin Mai’Adua, Alhaji Ahmad Diddiri Ahmad, ya yi wannan furucin a maimakon basaraken a ranar Alhamis, inda ya sanar da manema labarai cewa hakan ya na da alaka da taimakon da yake yi wa masarautar, Jihar Katsina da kasar baki-daya.

“Masarautar bata alakanta kanta da wata jam’iyya ba kuma za ta ba Amaechi sarautar ne saboda kokarin sa. “Mun lura da abubuwa biyu ne na tallafin da ya yi wa masarautar Daura, Jihar Katsina da kuma kasa baki-daya.

“Duk da halin da kasa take ciki, an yi Jami’ar Sufuri a nan Daura wanda hakan zai zama babbar hanyar kawo ayyukan yi ga mutanen mu.” Ya bayyana yadda Amaechi ya gina hanyoyin jirgin kasa da ya bi ta daura wannan ba ƙaramin cigaba bane.

Yadda aka yi titina biyu na jirgin kasa da ya shiga ta Daura wanda hakan zai taimaka wa hada-hadar kasuwancin jama’a, wanda ya wuce ta Jihar Kano zuwa Niamey har Dakar wanda mutane da dama za su amfana da shi.

Yayin da aka tambaye shi ko an bayar da sarautar ne saboda matsayin Amaechi a wurin Shugaba Buhari, Galadiman Daura cewa ya yi wannan surutai ne na mutane. A cewarsa, masarautar su bata da alakar siyasa da ko wacce jam’iyya kuma ba ta karrama wani akan dalilin siyasa.

A cewarsa da tsarkin niyya muka karrama shi Ya ce: “Niyya tsarkakakkiya muke da ita akan karramawar da muka yi masa, kuma mun yaba da kokarin sa ne don haka muke shirin kara masa kwarin guiwar ci gaba da yin hakan.

Labarai Makamanta