Masarautar Argungu Ta Nada Shugaban Majalisar Dattawa Sarautar Ganuwan Kabi

Mai martaba Sarkin Kabin Argungun dake Jihar Kebbi Alhaji Samaila Muhammadu Mera, a ranar Juma’a a ya nada Shugaban Majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan Sarautar Ganuwan Kabi.

Wannan nadi na cikin bukukuwan cikar Sarkin Argungun shekaru 25 kan karagar mulki, Ola Awoniyi mai magana da yawun Ahmad Lawan ya sanar da hakan.

Wadanda aka yiwa nadi kuma a bikin sune tsohon Gwamnan jihar Abia kuma mai tsawatarwa a majalisa, Orji Uzor Kalu(a matsayin Kibiyan Kabi), da kuma Shugaban kamfanin wutan lantarkin Kaduna KEDC, Engr Garba Haruna Argungu.

Wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnonin, Sarakunan gargajiya da kuma yan majalisar dokokin tarayya.

Daga cikin gwamnoni akwai Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni; da Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari.

Daga cikin Sarakunan gargajiya kuwa akwai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad III; Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero; da Mai martaba Sarkin Zazzau, Amb Bamalli.

Sauran sune Sarkin Bade, Sarkin Biu, Sarkin Machina, Sarkin Lafiya, Sarkin Zuru da Sarkin Zamfara.

Cikin yan majalisa kuwa akwai Sanata Barau Jibrin, Sanata Muhammad Musa Bello, Sanata Chukwuka Utazi, Yahaya Abdullahai, Sanata Shuaibu Lau, Sanata Michael Nnanji.

Labarai Makamanta