Masanin Yanar Gizo Ya Yi Tir Da Kisan ‘Yan Arewa

Wani Masanin yanar gizo kuma mai kirkiran shafuka na yanar gizo Aminu Iliyasu Kajuru yayi Allah wadai da Abun da yakira kisan kare dangi da ake yima yan Arewa mazauna kudu.

Aminu Kajuru wanda haifaffen dan Jahar kaduna ne kumar masanin yanar kizo yayi tirr da Allahwadai da ayyukan da matasa yarbawan kudu ke yima yan Arewa.

Kajuru yace baya goyan bayan kisa ko wani iri ne akowani yankin kasar.

Kajuru ya kuma kara da cewa yana mamakin irin yadda yarbawa masu daukan kansu amatsayin wa inda sukafi kowa ilimi a kasar Nijeriyya amma sai gashi sun tsunduma kansu cikin daukan doka ahannunsu da kuma hukunta wa danda ba sujiba basu gani ba.

Kajuru yayi kira da shuwagabanni da su hanzarta daukan mataki kafin lokaci ya kure musu. Daga karshe ya mika ta’aziyyarsa ga wanda abun yashafa yayi adu’ar Allah yakawo zaman lafiya akasar baki daya.

Labarai Makamanta