Masana’antar Kannywood Ta Wuce Tunanin Mai Tunani – Aminu Saira


Fitaccen Darakta a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Malam Aminu Saira ya yi kira ga masu gudanar da harkokin sana’ar su a cikin Kannywood da su mayar da hankali wajen yin sana’ar su, ta yadda masana’antar za ta tsaya da kimar ta kamar yadda sauran masana’antar fim take a kasashen Duniya.

Darakta Aminu Saira ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, a kan yadda a ke ganin harkar fim ta koma a yanzu.

In da ya ke cewa “Gaskiya harkar fim ko kuma in ce masana’antar ba ta komawa baya, sai dai kawai wanda ya mayar da kan sa baya, sai kuma ya ke ganin masana’antar ta koma baya.

Domin kuwa ita harkar rayuwa duk yadda ka dauke ta a haka za ka samu kan ka, don haka idan kana cikin kowacce harka to kai ne ka ke kai kan ka gaba, kuma kai ne za ka dawo da kan ka baya. ” Inji shi.

Ya ci gaba da cewa” Yanzu ka duba ai Masarautar ba mutuwa ta yi ba, ana yin fim, amma wanne irin fim a ke yi, wanda zai rike masana’antar ne ko sabanin haka? Ai muna da Kwarewa a kan harkar fim to me ya sa ba za mu yi amfani da Kwarewar mu ba? Ina tabbatar maka idan har muna da tsari duk wani fim da a ke yi a duniya, to za mu iya yin sa a wannan masana’antar, kayan aiki ne, kuma idan muka zuba kudi babu kayan aikin da ba za mu samar ba. Babu Maganar labari domin kowa ya san muna da labarai masu inganci wadanda idan aka yi fim da su duk duniya za su karbu, don haka abin da ya rage mana kawai shi ne tsari, in muna da tsari komai za mu iya yi. ”

Da ya juya kan fim din Labarana kuwa cewa ya yi” yanzu lokacin da muka fara aikin fim din Labarana ai ana ganin kamar asarar kudin mu mu ke yi saboda babu irin sa a masana’antar a lokacin, mu kuma muna da tsari muna kallon yadda aka koma fim mai dogon Zango a duniya, don haka muka ga ba za a bar mu a baya ba, don haka muka tafi da zamani, yau kuma ga shi kowa ya ga irin karbuwar da Labarina ya yi kuma ya sauya tsarin masana’antar, to ko wannan abin alfahari ne a gare mu da muka samar da tafiya da zamani a cikin masana’antar Kannywood. ”

Daga karshe ya Kara yin kira ga masu harkar fim da su rinka tafiya da zamani a duk lokacin da aka samu ci gaba a cikin harkar fim ta duniya.

Labarai Makamanta