Martani Ga Igboho: Mun Bada Awa 72 Ka Kwashe Yarbawa Daga Arewa – Matasan Arewa

Kungiyar Matasan Arewa ta AYA ta baiwa me ikirari kare muradun Yarbawa, Sunday Igboho awanni 72 ya kwashe yarbawa daga Arewa ko kuma su tursasa musu barin yankin.

Kakakin kungiyar, Muhammad Salihu Danlami ya bayyan cewa, zaman Najeriya a matsayin kasa daya ba abune na wasa ba, ya jawo hankalin jami’an tsaro da su yi watsi da duk wani abu da zai kawo tada hankali a kasar.

Kungiyar tace har yanzu ita kungiyar matasa ce me bin doka da oda wajan gudanar da ayyukanta, amma ba zata nade hannu tana kallo ana yiwa wasu ‘yan kasa Barazana ba.

Tace tunda Sunday Igboho na son kafa kasarsa, zasu saukaka mai hakan, ya aiko da motoci da zasu dauki mutanen nashi zuwa kudu.

Labarai Makamanta